Daga Auwal Alhassan Kademi
Shugaban Nigeria mai barin gado Muhammadu Buhari ya ce a yanzu ƴan Najeriya suna da damar neman bankunansu su rika ba su katin cirar kudi na ATM wanda yake hade da bayanan katin ɗan-ƙasa, wato na komai-da-ruwanka kenan.
Ministan ma’aikatar sadarwa Farfesa Isa Pantami, ne ya sanar da hakan a jiya Laraba a Abuja, inda ya ce babu wani kudi na daban da mutum zai biya a kan hakan.
Da dumi-dumi: Ganduje ya mika muhimman bayanan gwamnatin Kano ga Abba Gida-gida
Farfesa Pantami ya ce an samu amincewar yin hakan ne a lokacin taron majalisar zartarwa ta tarayya, wanda Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranta a Abuja.
Ministan ya ce an bayar da damar hakan ne sakamakon takardar da hukumar da ke yin katin dan-kasar ta gabatar ta neman a amince bankuna su rinka yin katin banki wanda kuma za a iya amfani da shi na a matsayin na dan-kasa.