Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Wata daliba da aka kwace wa waya a makaranta ta tayar da gagarumar gobara a dakin kwanan ‘yan uwanta dalibai a wata makaranta a Guyana, in ji hukumomi.
Mutane goma sha tara ne yawanci dalibai mata suka rasu a gobarar, a kasar ta Latin Amurka a cikin daren Litinin.
Dakin kwanan an ce yana kulle kuma duk tagoginsa na rufe, abin da ya hana daliban samun damar tserewa ke nan.
Dalibar ‘yar shekara goma sha ita ma wutar da kona ta inda yanzu take kwance a asibiti kuma rahotanni sun ce ta amsa cewa ita tayar da wutar.
Hukumomi na neman shawara kan ko za su tuhume ta da laifin tayar da gobarar, kamar yanda wani ya sheda wa kamfanin dillancin labaran AFP.
rahotanni sun ce gobarar ta fara ne daga wurin ban-daki sannan ta kama ginin gaba daya wanda na katako ne da ke dauke da dalibai 57 a lokacin.
Wadanda suka tsira da ransu a gobarar a garin Mahdia na tsakiyar kasar sun ce ihu da kururuwar da suka ji a cikin dare ne suka tashe su.
Bayanai sun nuna cewa yarinyar ta yi barazanar aikata abin bayan da aka hukunta ta saboda tana alaka da wani naiji babba wanda ya girme ta.
Yan kwana-kwana sun rika fasa tagogin ginin ne kafin su iya cetar wadanda suka tsira da rai.
Wasu daliban sun kone sosai ta yadda sai an yi gwajin kwayoyin halitta kafin a iya gane gawarwakin.
Shugaba Irfaan Ali da farko ya bayyana lamarin a matsayin babban bala’i.