Yadda jarirai suka mutu a asibiti sanadiyyar yanke wutar lantarki

Date:

Daga Nasiba Rabi’u Yusuf

 

An dawo da wutar lantarki a wani asibiti da ke arewacin kasar Ghana, abin da ya faranta wa wani likita rai wanda ya ce jarirai biyu sun rasu bayan kamfanin wutar lantaki na gwamnati ya yanke wa asibitin wuta a farkon watan nan.

Dr Gbeadese Ahmed wanda ke asibitin St Anne da ke Damango, ya shaida wa BBC cewa ya na shirin komawa tiyata domin ya cigaba da ayyukan da aka dakatar na tsawon kwanaki bakwai.

Ya ce, ɗan majalisar yankin wanda kuma minista ne a gwamnati, Abdulai Jinapur ya biya wasu basuskan da kamfanin wutar lantarkin ta Nedco ke bin asibitin.

Agajin da ɗan siyasar ya kawo ya biyo bayan tattaunawa da Dr Ahmed ya yi da tashar Citi news ranar Liltinin a kan yadda yanke wutar lantarkin ya sanya asibitin cikin mawuyacin hali a garin wanda ke da nisa kilomita 630 daga babbn birnin kasar, Accra.

Ya yi bayanin cewa jarirai biyu sun rasu kuma wasu jarirai uku na cikin mawuyacin hali saboda rashin wutar ya hana ma’aikatan asibitin yi wa jariran ƙarin jini.

An fara samun matsala a asibitin ne a ranar 4 ga watan Mayu lokacin da aka fara yanke wutar sakamakon bashin sama da $370, 000 da ake bin ta.

A lokacin ne jaririn farko ya rasu, a cewar Dr Ahmed.

Tun farkon watan Mayu kamfanonin rarraba wutar lantarki na Ghana suka fara matsa lamba kan marasa biyan kuɗin wuta a ƙoƙarin da su ke yi na karbo miliyoyin kuɗi da su ke bi bashi.

An yanke wa ma’aikatun gwamnati da dama wuta sakamakon rashin biyan kuɗin wutar lantarki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Shugabannin Hukumomi a Kano Sun Yaba Da Ayyukan Abba, Sun Nemi Ya Nemi Wa’adi Na Biyu

Kungiyar shugabannin hukumomi da ma'aikatun gwamnatin jihar Kano ta...

Idan mu ka rungumi Addu’o’i ba abun da Amurka za ta iya yiwa Nigeria – SKY

Shahararren ɗan kasuwa a Kano, Alhaji Kabiru Sani Kwangila...

Shugaban APC na Kano Abdullahi Abbas ya Magantu Kan Zargin raba Ramat da Kujerarsa

Shugaban jam’iyyar APC na Jihar Kano, Alhaji Abdullahi Abbas,...

Iftila’i: An tsinci gawar wata dattijuwa mai shekaru 96 cikin rami masai a Kano

A ranar Alhamis al’ummar ƙauyen Sarai da ke ƙaramar...