Daga Rahama Umar Kwaru
Gwamnan jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana na’urorin zamani a matsayin wadanda suke taimakawa wajen magance aiyukan bata gari, Saboda cigaban da aka samu .
” Saboda cigaban zamani da aka samu a duniya yasa gwamnatin mu ta samar da na’urorin zamani domin dakile aiyukan bata gari da Kuma kama Masu laifi a jihar Kano , wanda hakan yasa muka Sami nasarorin da muka samu a tsahon shekaru 8 na mulki na”. Inji Ganduje
Shafukan sada zumunta na da hadari ga lafiyar matasa – Masana
Gwamna Ganduje ya bayyana hakan ne lokacin da yake jawabi yayin bude sabon ofishin yan sanda dake unguwar Rijiyar Zaki a karamar hukumar Ungoggo a Kano.
Ganduje wanda Sakataren gwamnatin jihar kano Alhaji Usman Alhaji ya wakilta ya yabawa Shugaban karamar hukumar Ungoggo Abdullahi Garba Ramat saboda kokarin da yake na bada gudunmawa don inganta tsaro a yankin da jihar kano baki daya.
Ya bukaci jami’an yan sanda da zasu aiki a sabon ofishin yan sandan na zamani da su yi amfani da Sabbin na’urorin da aka Sanya yadda ya dace don cigaba da samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar.
A jawabinsa tun da fari Shugaban Karamar Hukumar Ungoggo Abdullahi Garba Ramat ya ce bayan gini na zamani da aka yiwa ofishin yan sandan, an Sanya na’urorin zamani don saukaka aiyukan yan sanda da kuma magance matsalolin tsaro a yankin.
Sh ma a nasa jawabin kwamishinan yan sanda na jihar kano CP Muhammad Usaini Gumel ya yaba da Samar da sabon ofishin yan sandan, tare da bada tabbacin zasu yi kyakyawan amfani da na’urorin domin dakile aiyukan bata gari a yankin da kana baki daya.