Shafukan sada zumunta na da hadari ga lafiyar matasa – Masana

Date:

Wani babban jami’in lafiya a kasar Amurka ya fitar da gargadi kan hadarin shafukan sada zumunta ga yara da matasa.

Dr Vivbek Murthy, wanda shi ne shugaban ma’aikatar lafiya ta Amurka ya ce kafofin sada zumunta da muhawara da kananan yara da matasa ke amfani da su na haifar da manyan kalubale ga lafiyar jiki da rayuwarsu.

Sannan suna haddasa matsalar rashin cin abinci da jefa masu amfani da su cikin damuwar rashin yarda da kai.

BBC Hausa ta rawaito Rahoton ya ce matakan da ake dauka domin rage damar da yara ke da ita ko matasa a shafukan sada zumunta ba sa aiki.

Sannan kuma akwai sauran jan aiki a binciken gano cikakken tasirin da wadannan shafuka ke yi a rayuwar matasa.

Sai dai kuma duk da wannan gargaɗi masanin ya ce akwai wasu alfanu da waɗannan shafuka kan yi ga wasu rukuni na mutane a rayuwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Zargin Almundahana: ICPC zata gurfanar da shugaban hukumar zabe ta Kano da wasu mutum biyu

    Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta (ICPC)...

Dalilin da ya hana ni zuwa Kano tarbar Tinubu – Ganduje

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa,...

Shugaban RATTAWU na Kano ya taya sabbin shugabannin kungiyar na kasa murna

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Shugaban kungiyar ma’aikatan rediyo, Talabijin da...

Dalilina na ziyartar gwamnan Kano Abba – Inuwa Waya

Daga Rahama Umar Kwaru Tsohon Wanda ya nemi Zama Dan...