Hukumar lafiya ta duniya, WHO ta ce cutar kwalara ta barke a kasashen Afirka guda 15 ciki har da Afirka ta Kudu.
A ciki akwai kuma Jamhuriyar Dumukuradiyyar Kongo (DRC) da Eswatini da Mozambique da Kenya da kuma Zimbabwe.
Hukumar ta bayyana hakan ne bayan da mutum 15 ciki har da karamin yaro dan shekara uku suka mutu a Afirka ta Kudu a sanadiiyar kamuwa da cutar wadda ta fara mako daya da ya wuce.
Akwai kuma wasu mutanen sama da 30 da ke kwance a asibiti a cikin mawuyacin hali a kasar ta Afirka ta Kudu.
Hukumar ta WHO ta kuma ce Malawi ce ta fi yawan mutanen da suka kamu da cutar.
Su kuwa hukumomin Afirak ta Kudu sun ce an dauki tsauraran matakai a iyakokin shiga kasar domin hana masu dauke da cutar shiga.