Daga Safiyanu Dantala Jobawa
Shugaba Joe Biden, na Amurka ya bayyana sunayen wakilan gwamnatinsa da za su haraci rantsar da sabon shugaban Najeriya mai jiran-gado, Bola Tinubu, ranar Litinin 29 ga watannan na Mayu a Abuja.
A wata sanarwa daga Biden wadda aka sanya a shafin intanet na fadar gwamnatin Amurkar, White House jiya Litinin da daddare, shugaban ya sanar da tawagar mutum tara da za ta halarci taron.
Tawagar ta Amurka za ta kasance karkashin jagorancin Ministar Gidaje da Raya Birane, Marcia L. Fudge.
Ana sa ran halartar shugabannin kasashen duniya na da da wadanda ke kan mulki da jami’an diflomasiyya da shugabannin hukumomin duniya da wakilan gwamnatocin kasashe.
Za a rantsar da Tinubu tsohon gwamnan jihar Lagos a matsayin shugaban Najeriya na 16, a ranar ta 29 a dandalin taro na Eagle Square da ke Abuja
Tun daga ranar Alhamis za a fara gudanar da bikin inda Shugaba Muhammadu Buhari mai barin-gado zai bai wa Tinubun lambar girmamawa mafi girma ta Najeriya wato GCFR (Grand Commander of the Order of the Federal Republic) wadda ake ba shugaban kasa, sai kuma mataimakinsa Kashim Shettima wanda za a ba shi lambar da ke bi mata ta GCON ( Grand Commander of Order of the Niger).