Daga Auwal Alhassan Kademi
Tsohon shugaban kasar Nigeria Goodluck Jonathan ya ce rashin tsaro ya sa shi “mummunan ciwon kai” a lokacin da yake rike da shugabancin Najeriya.
Ya bayyana haka ne a lokacin kaddamar da aikin titin mai tsawon kilomita 22 a jihar Taraba.
A cewarsa, yana kwana bai yi barci ba sakamakon kokarinsa na magance matsalar tsaro a wancan lokaci.
Tsohon shugaban kasar ya bukaci al’ummar jihar da su zauna lafiya domin a samu ci gaba.
Jonathan, wanda ya bayyana cewa tsaro yana hannun jama’a, ya bayyana farin cikinsa yadda a hankali Taraba ke komawa cikin kyakkyawan yanayin zaman lafiya da juna.
“Lokacin da nake shugaban Najeriya, rashin tsaro ya sa na kasa barci. Wani lokaci ma yayin da nake coci, ADC na ya kan kawo waya ta ya nuna min yadda ake kashe mutane ko sace mutane, kuma hakan yana da na sami ciwon kai kuma na kasa barci.”
“Lokacin da na shigo filin jirgin sama na Jalingo, da na ga Daraktan DSS, sai na yi sauri na tambaye shi, ‘Yaya akai jami’an tsaron jihar Taraba suke da himma?’ sai ya ce min mutanen ‘Taraba na son zaman lafiya da kwanciyar hankali’,” a cewar Jonathan
Jonathan ya zama shugaban Najeriya daga 2010 zuwa 2015