Daga Rukayya Abdullahi Maida
Shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai, Alhassan Ado Doguwa ya janye kudirinsa na neman shugabancin majalisar wakilai ta 10, Inda ya bayyana goyon bayansa ga Tajudeen Abbas.
Doguwa ya jagoranci wasu ‘yan takara biyu Abubakar Makki da Tunji Oluwuyi, inda suka janye daga takararsu a ranar Larabar da ta gabata yayin wani taro da kungiyar hadin gwiwa ta shirya, kamar yadda rahoton Daily Post ya nuna.
Da dumi-dumi: Tinubu zai zo Kano domin kaddamar da wasu aiyuka – Ganduje
Idan dai ba a manta ba kadaura24 ta rawaito jam’iyyar APC mai mulki ta amince da Abbas da Ben Kalu a matsayin shugaban majalisar da mataimakinsa, lamarin da ya haifar da cheche-ku ce a tsakanin ‘yan takarar.
A baya dai Doguwa ya bi sahun wasu masu kalubalantar Abbas, Amma kuma yanzu ya aminta zai marasa masa baya.