Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Gwamnan jihar kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya mayar da kakkausan martani ga masu zargin sa da cewa ya sayar kaddarorin gwamnatin jihar kano.
Ida za’a iya tunawa a makon da ya gabata kadaura24 ta rawaito cewa, Shugaban kwamitin karɓar mulki na jam’iyyar NNPP Abdullahi Baffa Bichi, ya zargi gwamnatin Ganduje da yasar da gidaje da kaddarorin gwamnatin ga wasu shafaffu da Mai.
Abba Gida-gida ya nemi al’ummar Kano su taimaka masa da bayanai kan gwamnatin Ganduje
Gwamna Ganduje ya bayyana hakan ne yayin da ya jagoranci bude sabon ginin ma’aikatar matasa da wasanni ta jihar kano.
” Na ji wani yana cewa wai ana sayar da gidaje, to Ina so ya sani gwamnatoci baya ma sun sayar, Kuma idan bashi da masaniya ya zo in nuna masa gidajen da mai gidan sa ko kakansa a siyasa ya siyar, da kuma wanda babansa a siyasance ya sayar.
Gwamna Ganduje ya yi suka Mai kaushi kan wannan batu na sayar da gadaje Inda yace Kwankwaso ma yayi Kuma ba laifi ba ne a gwamnatance.