Zaben gwamnan kano: Inda aka Kwana game da karar APC da NNPP a Kotu

Date:

Daga Sani Idris Maiwaya

 

Jam’iyyar NNPP reshen Kano a jiya litinin ta gabatar da martaninta kan karar da jam’iyyar APC ta shigar a gaban kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan Kano.

 

A baya dai kadaura24 ta rawaito cewa mai kara wato jam’iyyar APC ta nemi kotun ta bayyana cewa NNPP ba ta da dan takara, inda suka ce Abba Yusuf ba ya cikin rajistar da jam’iyyar ta mika wa INEC a lokacin zabe kuma ta tabbatar da Nasiru Yusuf Gawuna a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan Kano da aka gudanar a ranar 26 ga Maris, 2023.

Mai shigar da karar ta kuma nemi kotun da ta bayyana APC a matsayin wacce ta lashe zaben bayan da ta samu mafi yawan kuri’un da aka kada idan aka cire kuri’un bogi a cikin kuri’un NNPP.

Zamu bar Gwamnatin kano na dan lokaci kafin mu dawo – Ganduje

A zantawarsa da ’yan jarida a harabar kotun, jim kadan bayan ya gabatar da karar, guda cikin lauyoyin da zasu tsayawa Abba Kabir Yusuf da NNPP, Barista Bashir Yusuf Muhammad ya ce bai kamata ya ce komai ba saboda batun yana gaban Kotu.

 

Sai dai ya nanata cewa tunda abin da ke gaban kotun na jama’a ne, yana da muhimmanci ya fadi halin da ake ciki don kauce wa yada labaran karya kan abin da ke faruwa a kotun sauraren kararrakin zaben na Kano.

 

Ya ce koken da jam’iyyar APC ta shigar gaban kotun ya riga ya mutu tun a tashin fari saboda bashi da tushe ballantana makama.

Akwai fargabar karatun daliban da dama a Jami’ar Yusuf Maitama Sule ya Sami tasgaro – Shugabar Dalibai

Lauyan ya yi nuni da cewa, Abba Kabir Yusuf da NNPP sun amsa karar ne da dalilai 34 wanda a cewarsa, kowane daya daga cikinsu ya Isa ya rushe duk bukatun da APC ta je da su (Kotun).

Barista Muhammad ya yi zargin cewa karar da jam’iyyar APC ta shigar, na kalubalantar nasarar Abba Kabir ba ta da amfani, bata lokaci ne kawai.

 

“Duk da cewa doka ta ba jam’iyya damar shigar da kara amma dan takararta ma ya kamata ya shiga cikin karar .

 

“ Kotu ba za ta iya karɓar bukata ko rokon wanda baya neman komai a gaban kotu .

 

“Idan kuka dubi korafinsu su na neman a bayyana dan takarar su a matsayin wanda ya lashe zaben ko kuma a sake gudanar da zaɓen bayan kuma baya cikin masu kara, saboda haka kotu ba ta da hurumin amincewa da bukatar a gare shi.”a cewar Lauyan

 

Lauyan ya kara da cewa karar mai dauke da bukatu guda 5 guda daya ce kawai zata take da hurumi sauran 4 na shedu ne domin su ya kamata su zo su goyi bayan kokensu.

 

Ya kuma jaddada cewa APC ba zasu razana su da yawan mujallen da aka shigar da karar na, illa iya ku zamu yi abun daya dace ne kamar yadda ya dace.

Justice Watch News

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin gida: Jam’iyyar APC ta Fara Tuhumar Kakakinta na Kano Ahmad S Aruwa

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jam'iyyar APC ta Mazabar Daurawa a...

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...