Daga Rukayya Abdullahi Maida
Gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje na jihar kano yace za su bar mulkin Kano na dan karamin lokaci kafin su sake dawowa .
” Wannan titi an kammala shi kuma mun zo budewa, budewar da muka sawa suna budewar bankwana, bankwana domin wannan yana cikin aiyukan da zamu bude domin mu yiwa mutanen kano bye-bye, amma na dan karamin lokaci”. Ganduje
Gwamna ya bayyana hakan ne lokacin da yake bude sabon titin kwanar Dala dake karamar hukumar Dala kano a yau din nan.
“Tarihi zai maimaita kansa na Dawo-dawo dama wancan Dawo-dawon ma mun muka sa aka yi ta, Kuma mu muka San Dawo-dawo, don haka a wannna lokaci kada mu manta da wakar nan ta Dawo-dawo”. Inji Gwamna Ganduje
Ganduje ya kuma bude tituna guda uku da suka hadar da titin Bello Kano terrace sai titin Kwanar Dala da Kuma na babban layi Kurna asabe da ke karamar hukumar Dala.