Daga Maryam Abubakar Tukur
Wata gwamnar girki a Najeriya, mai suna Hilda Effiong Bassey, da aka fi sani da Hilda Baci ta kafa tarihin girki a duniya, bayan shafe tsawon sa’o’i 87 da mintuna 50 tana girke a tsaye.
Hilda mai shekara 27, ta shafe wuni hudu tana girke domin kafa tarihin zarta Lata Tondon ta Indiya da ta shiga kundin tarihin bajinta na Guinness World Record.
Lata a shekara ta 2019 ta shiga kundin Guinness bayan shafe sa’o’i 87 da minti 45 tana girki a tsakiyar Indiya.
Bajintar da Hilda ta nuna a yanzu ya zarta na Lata, sai dai a hukumance ba a sanar da shigar da ita kundin Guinness ba.
Burin Hilda na kafa tarihi ya samu goyon-baya da yabo a shafukan sada zumunta.
An yi ta wallafata da nuna girkin nata kai-tsaye a shafukan sada zumunta, wanda milyoyi musamman a Instagram suka kalla.
An gudanar da gasar girkin ne a birnin Legas.