Daga Aisha Aliyu Umar
Karatun wasu daga cikin daliban jami’ar Yusuf Maitama Sule zai iya tsaya, sakamakon gaza biyan kudin makarantar da aka saba biya duk shekara a sabon zangon karatu.
“Mun karɓi koken dalibai da dama wadanda yawancinsu ‘yan aji uku da aji hudu ne cewar sun yi iya bakin kokarinsu domin su biyan kudin makarantar Amma abun ya ci tura, kuma babu shakka duk wanda aka rufe bai biya kudinsa akwai yiwuwar ya shiga wani hali maras dadi sakamakon dakatar da karatunsa”.
Shugabar kungiyar dalibai ‘yan asalin jihar kano dake karatu jami’ar Amb. Habiba Usman Hassan ce ya bayyana hakan yayin wata ganawa da ta yi da kadaura24.
Sarkin Karaye ya sake baiwa kanin Kwankwaso Sarauta
Tace dalibai da dama a baya sun shiga cikin mawuyacin hali sakamakon dakatar da karatunsu , hakan ce tasa ta ga dacewar a matsayinta ta shugaba ta nemar musu tallafi daga al’ummar jihar kano don inganta rayuwar su da kuma kare rayuwar su daga rugujewa.
“Gaskiya Hukumar jami’an ta yi iya kokarin ta domin ta karawa ɗaliban wa’adi, amma duk da haka akwai dalibai da dama da suka gaza biyan kudin, don haka muke rikon shugabanni da masu hannu da shuni da su tallafawa wadannan dalibai don ceto rayuwar su”.inji Amb. Habiba Usman Hassan
Amb. Habiba Usman wadda ake yiwa lakabi da Garkuwar dalibai tace idan aka sami Masu taimakawa Wadancan dalibai zasu iya tuntubar hukumar jami’ar ko kuma kungiyar dalibai yan asalin jihar kano domin ganin an tallafawa wadanda abun ya shafa.