Daga Mukhtar Dahiru
Jam’iyyar APC ta dakatar da wasu da ake zargin makusantan kakakin majalisar dokokin jihar Kaduna, Rt. Hon. Yusuf Zailani bisa laifin yiwa zababben gwamnan Kaduna malam Uba Sani zagon kasa a lokacin zaben gwamna wanda aka gudanar a ranar 18th ga watan Maris, 2023.
Wannan sanarwa na kunshe ne cikin wata takarda mai dauke da sa-hannun shugaba da sakataren jam’iyyar APC na mazabar Rigachikun a karamar hukumar Igabi Ali Isa da Abubakar Isa, wacce aka raba ta ga manema labarai yau Lahadi a jihar Kaduna.
Sanarwar ta ce bayan kwamitin ladabtarwa ya gudanar da bincike kan abubuwan da su ka aikata, ya same su da laifin cin amanar jam’iyyar APC a lokacin zaben 2023.
Sarkin Karaye ya sake baiwa kanin Kwankwaso Sarauta
Wadanda jam’iyyar APCn ta dakatar sun hadar da Aliyu Yusuf Councillor, Tanimu Jibrin, Abubakar Abdullahi, Al’amin Muhammad Saminu, Shehu Police Kurmin Kaduna, Mahrazu Ibrahim Kurmin Kaduna da kuma dan uwan Kakakin majalisar dokokin ta jihar Kaduna Manniru Ibrahim Zailani bisa laifin yiwa jam’iyyar APC zagon kasa.
Sauran ma su laifin sun hadar da Auwal Ibrahim, Rakiya Ya’u, Hajiya Hadiza, Rabi Adamu, Sa’idu Abubakar, Nasiru Alhaji Babba, Bello Isyaku da Mukhtar NDC.
Jam’iyyar ta APC a mazabar Rigachikun ta ce; ta dakatar da wadancan mambobi na ta ne dogaro da sashe na 21A (i & !!) cikin baka na kundin tsarin mulkin jam’iyyar APC na shekarar 2014. Wanda ya ba da dama a ladabtar da duk wani dan jam’iyyar APC da ya saba dokar jam’iyyar ko aka same shi da laifin cin amana da kuma yi mata zagon kasa.