Ma’aikatan jihar Zamfara sun gudanar da alqunut kan rashin biyansu albashi

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

 

A karshen makon ne dai daruruwan ma’aikatan jihar Zamfara suka mamaye filin Sallar Idi da ke Gusau babban birnin jihar domin gudanar da addu’a ta musamman (AlQunut) kan rashin biyansu albashin watanni uku.

 

Ma’aikatan sun mamaye filin Idi ne da misalin karfe 10:00 na safiyar ranar Asabar domin yin addu’o’in Allah yasa gwamnatin jihar ta biya su hakkokin su.

Wani ma’aikacin gwamnati da ya nemi a sakaye sunansa, wanda ya yi magana a madadinsu ya ce ba a biya ma’aikata albashin watanni Fabrairu, Maris da Afrilu ba .

Sarkin Karaye ya sake baiwa kanin Kwankwaso Sarauta

Ya ce suna rokon Allah ya magance musu matsalar rashin biyan ma’aikatan gwamnatin jihar da ‘yan fansho hakkokin su ba .

“Da yawa daga cikinmu ansa mun fara barace-barace, ba mu iya cin abinci sau uku a rana da kuma kasa biyan kudin makarantar ‘ya’yanmu”. Yace

An gudanar da alqunutin ne Allah yasa mai girma gwamna, shugaban ma’aikata, ’yan majalisar tarayya, da duk wanda abin ya shafa, Allah ya ba su ikon tausaya mana.

“Mun sha wahala sosai a wadannan watanni, da yawa sun mutu, kuma ba ma Jin dadin hakan.

Ya kara da cewa “Mun taru ne baki daya ba tare da banbancin addini ba don neman taimakon Allah ga kowa da kowa a cikin mu.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rasuwar Buhari: Majalisar Nigeria ta dakatar da duk aiyukanta

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Majalisar dokokin Nigeria ta dage zamanta...

Gwamnati ta baiwa ma’aikata hutu saboda rasuwar Muhammad Buhari

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Gwamnatin jihar Katsina karkashin gwamna Umar...

Bayan tura Kashim ya taho da gawar Buhari, Tinubu ya ba da umarnin sassauta Tutar Nigeria

Shugaban kasa Bola Tinubu ya bada umarnin ayi kasa...

Yanzu:yanzu: Tsohon shugaban Nigeria Buhari ya rasu

Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un!!! Allah yayi wa tsohon shugaban...