Makiyaya sun kashe zakuna shida da suka addabi ƙauyensu

Date:

Wasu Makiyaya sun kashe wasu zakuna shida a gundumar Kajiado na ƙasar Kenya, bayan da zakunan suka kwashe tsawon daren Asabar suna far wa mazauna ƙauyen Nashipa.

 

Rahotonni sun ce zakuna 11 da suka tsere daga gandun dajin ‘Amboseli National park’, suka afka wa ƙauyen tare da addabar al’ummar ƙauyen na tsawon dare guda.

Sarkin Karaye ya sake baiwa kanin Kwankwaso Sarauta

Zakunan sun yi ta far wa gidajen mutane inda suka kashe tumaki 11 tare da kare guda, a wani lamari da wani mazaunin ƙauyen ya bayyana da ‘daren subhana’.

“Yunkurin da masu tumakin suka yi na ƙubutar da su ya ci-tura, tumaki ne da suka tsallake-rijiya-da-baya daga masifar fari da ƙasarmu ke fuskanta, amma sai ga shi sun ƙare a matsayin kalacin zakuna,” in ji wani mazaunin ƙauyen.

BBC Hausa ta rawaito cewa a ranar Asabar da safe ne gwamman mazauna ƙauyen suka ɗauke da kwari da baka da wasu makaman suka ƙaddamar da farautar zakunan tare da kashe shida daga cikinsu.

Jami’an kula da gandun dajin ƙasar da jagororin kauyen da sauran masu ruwa da tsaki sun gudanar da ganawar gaggawa kan lamarin da maraicen ranar Asabar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bai dace ɗalibai su rika murnar kammala karatu ta hanyoyin da ba su dace ba – Mal Ibrahim Khalil

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa ‎ ‎ ‎Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano...

Budaddiyar Wasika ga Gwamnan Kano kan wanda zai maye gurbin Muhuyi Magaji R/gado daga Kungiyar Lauyoyi yan Kano

Zuwa ga Mai Girma Alhaji Abba Kabir Yusuf Gwamnan Jihar Kano Gidan...

Dan majalisa Bichi ya sake biyan kuɗin makarantar dalibai 121 masu karatun digiri na biyu da na digirin digirgir

Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Mazabar Bichi a Majalisar...