Daga Maryam Ibrahim Muhammad
Fadar shugaban kasa ta ce ba ta da masaniya kan matakin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dauka na bai wa gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele hutun karo karatu.
Jaridar Sahara Reporters ce dai ta rawaito cewa Shugaban kasa Muhammad Buhari ya amince gwamnan babban bakin ya tafi hutun karo karatu.
Babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Malam Garba Shehu, ne ya bayyana haka a lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai a ranar Lahadi.
Sarkin Karaye ya sake baiwa kanin Kwankwaso Sarauta
“Idan har gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, ya samu amincewar Shugaban kasa Muhammad Buhari na ya tafi hutun karo karatu to ba mu da masaniya akan hakan ba”. Garba Shehu
Yadda wata bazawara ta yi Garkuwa da ‘yarta don neman kuɗin shiga Fina-finan Hausa a kano
“Haka zalika sakatariyar shugaban kasa karkashin jagorancin shugaban ma’aikatan fadar ba.”
Emefiele dai ya yi yunkurin samun tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC mai mulki, Tinubu ya zarge shi da fito da tsarin sauya fasalin wasu daga cikin kuɗaɗen Nigeria don yi masa zagon kasa.