Daga Umar Ibrahim Kyarana
Mai Martaba Sarkin Karaye Alhaji Dr. Ibrahim Abubakar II ya baiwa Alhaji Umar Musa Kwankwaso sarautar Majidaɗin Masarautar Karaye.
Umar Musa Kwankwaso kane ne ga jagoran jam’iyyar NNPP Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in yada labaran Masarautar Karaye Haruna Ganduwawa ya aikowa kadaura24.
Matashin nan da ya auri baturiya yar a Kano ya zama soja a Amurka
Marigayi Sarkin Kano Alhaji Dr. Ado Bayero ne ya fara nada mahaifinsa Umar marigayi Alhaji Musa Saleh Kwankwaso a matsayin Majidaɗi kano kuma Hakimin Kano na Madobi, sannan daga bisani ya zama Makaman Karaye Hakimin Madobi,kuma guda cikin masu nada Sarki a Masarautar Karaye. sannan kuma Shugaban Kwamitin Dattawan Masarautar wanda Mai Martaba Sarkin Karaye Alhaji Dr Ibrahim Abubakar II ya nada shi.
Ba maniyacin da zai biya karin kuɗin aikin Hajjin bana – NAHCON
Za a nada Sabon Majidaɗi na Karaye Alhaji Umaru Musa Kwankwaso da sauran mutane goma sha daya da za a nada a ranaku biyu ranar 19 da 26 ga Mayu 2023.
Wadanda za a nada a ranar 19 ga watan Abdulkadir Muhammad Bature a matsayin Fagacin Karaye, Lawan Sule Garo a matsayin Galadiman Garon Karaye, Garba Musa Ajiya a matsayin Ajiyan Karaye, sakataren masarautar Karaye Tijjani Usman Getso a matsayin Dan-adalan Karaye, Ali Surajo Karaye a matsayin Bunun Karaye da Badamasi Sulaiman a matsayin Uban Doman Karaye.
Rukuni na biyu kuma na ya haɗar da Umar Musa Kwankwaso a matsayin Majidaɗin Karaye, tsohon Daraktan hukumar wayar da kan jama’a ta jiha Dr. Ayuba Ibrahim Adamu a matsayin Dokajin Karaye, shugaban karamar hukumar Gwarzo Injiniya Bashir Abdullahi Kutama a matsayin Dallatun Karaye, Isa Iliyasu a matsayin Katukan Karaye da Injiniya Nasiru Yakubu Beli a matsayin Yan Ɗakan Karaye za a nada su a ranar 26 ga Mayu 2023.