Daga Rukayya Abdullahi Maida
Majalisar dokokin Najeriya ta fara shirya wa yi wa sababbin zaɓaɓɓun ‘yan majalisar dattawan majalisa ta 10 bitar ayyukan majalisar.
Bitar za ta taimaka wajen ilimantar da zaɓaɓɓun ‘yan majalisar wajen sanin makamai aikin majalisar.
Cibiyar kula da ayyukan majalisa da dimokradiyya a ƙasar ta ce bitar na da matuƙar muhimmanci kasancewar fiye da kashi 70 cikin 100, na zaɓaɓɓun ‘yan majalisar, karon su na farko kenan da suke zuwa majalisar.
Kotun sauraren kararrakin zaben shugaba ta bada tabbacin yi wa kowa adalci
Daga kano Hon. Sulaiman Abdulrahman Kawu Sumaila na jam’iyyar NNPP na daga cikin sabbin zababbun sanatoci da suka halarci taron.
A cikin watan Yuni mai zuwa ne za a rantsar da majalisar wadda ita ce ta 10 a Najeriya.