Daga Safiyanu Dantala Jobawa
Kotun sauraron ƙorafe-ƙorafe kan zaɓen shugaban kasa ta fara zama a yau Litinin.
An fara zaman ne da misalin ƙarfe 9:15 na safe, inda alƙalin da ke jagorantar zaman kotun, mai shari’a Haruna Tsammani ya gabatar da jawabi.
Tsammani ya ce kotun za ta yi masu ƙarar adalci sannan ya gargaɗi lauyoyi da su guje wa yin kalamai na harzuƙawa.
Bankwana: Ganduje ya yafewa malaman makaranta kudaden gidaje
Ya kuma buƙace su da su bai wa kotun haɗin kai domin ganin an kammala shari’ar cikin lokacin da aka ɗiba.
Sauran alƙalan da za su taimaka wajen gudanar da shari’ar sun haɗa da mai shari’a Stephen Adah da Misitura Bolaji-Yusu da Boloukuoromo Moses Ugo da kuma Abbah Mohammed.
Gabanin fara zaman, an jibge jami’an tsaro a kan hanyoyin da suke kai wa zuwa kotun.
Jam’iyyun adawa irin su PDP da LP ne suka shigar da ƙara suna ƙalubalantar nasarar da ɗan takarar jam’iyyar APC mai mulki, Bola Tinubu ya samu a zaɓen shugaban ƙasa na 2023.
Kadaura24 ta rawaito Sakamakon da INEC ta fitar ya nuna cewa Bola Tinubu na APC ya samu ƙuri’u 8,794,726, sai Atiku Abubuakar na jam’iyyar PDP wanda ya samu ƙuri’a 6,984,520, yayin da Peter Obi na jam’iyyar LP ke biye masu da ƙuri’a 6,101,533.