Inganta aikin Hisbah: Ganduje ya yabawa Shekarau Kwankwaso

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

 

Gwamnan Jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya yabawa gwamnonin kano da suka gabata bisa yadda suka inganta aikin hukumar Hisbah ta jihar kano.

” Duk gwamnonin demokaradiyya da suka yi mulki a Kano dole a yaba musu saboda yadda suka karfafi hukumar Hisbah a zamanin su, Inda hakan ce tasa muma muka yi iya kokarin mu don samar da kayan aiki da kuma karfafa hukumar a zamanin mulki na”. Inji Ganduje

 

Gwamna Ganduje ya bayyana hakan ne lokacin da yakai ziyarar ganin aiyukan da ake yi a cikin helkwatar hukumar ta Hisbah dake Sharada a kano.

Da dumi-dumi: Allah kadai yasan jam’iyyar da zan mikawa mulkin Kano – Ganduje

Ya ce yana fatan gwamnatin da za ta gajeshi zata karawa hukumar karfi don ta cigaba da aikin ta na hani da mummunar da Kuma umarni da kyakyawa.

 

” Mun gudanar da aiyukan Masu tarin yawa a wannan hukuma ta hanyar yin sabbin gine-gine da kuma samar da ababen hawa don inganta aiyukan hukumar”.

 

Gwamna Ganduje ya kuma baiwa hukumar Umarnin farfasa kwalaben giya Masu tarin yawa wadanda aka kamasu yayin da aka shigo da su jihar kano. Ya kuma yabawa al’ummar jihar bisa hadin kan da suke baiwa hukumar Hisbah ta jihar kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Wata sabuwa: Sanata Barau Jibrin ya gana da Baffa Bichi da Muhd Diggol

Tsohon sakataren gwamnatin Jihar Kano Dakta Abdullahi Baffa Bichi...

Rikicin Masarautar Kano: Kotu ta Sake Sabon Hukunci

A wani sabon yanayi na rikicin Masarautar Kano, Kotun...

Gidauniyar Aliko Dangote za ta rabawa ‘yan Najeriya miliyan daya shinkafa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Gidauniyar Aliko Dangote ta raba buhunan...

Rufe Makarantu da azumi: Ministan Ilimi ba ta da ilimin harkokin mulki – Jafar Sani Bello

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Tsohon dan takarar gwamnan jihar Kano...