Zargin kisan kai ba zai hanani neman shugabancin majalisar wakilai ba — Doguwa

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

 

Shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai, Alhassan Ado Doguwa, ya bayyana cewa shari’ar zargin kisan kai da ake yi da shi ba za ta hana shi neman kujerar shugaban majalisar wakilai ta 10 ba.

Daily Nigeria ta rawaito Da ya ke magana a wajen sanar da takararsa ta shugaban majalisar a jiya Laraba a Abuja, dan majalisar ya dage cewa ba shi da wani laifi har sai kotu ta tabbatar da laifinsa ko akasin haka.

 

Jaridar Kadaura24 ta ruwaito cewa Doguwa na fuskantar shari’a kan tuhumar da ake masa na kisan kai, mallakar bindiga ba bisa ka’ida ba, da dai sauransu, a babbar kotun tarayya da ke Kano.

Da dumi-dumi: Allah kadai yasan jam’iyyar da zan mikawa mulkin Kano – Ganduje

“Ina son ƴan Nijeriya da abokan aikina su kasance tare da ni wajen yin addu’a domin da yardar Allah gaskiyar lamarin za ta bayyana.

 

“Dole ne in jaddada cewa wanda ake tuhumar shi da irin wannan laifi amma ya shiga zaɓen cike gurbi kuma ya yi nasara.

“Na koma wurin mutanen Tudun Wada, gabatar da kaina. Na yi zaben cike-gurbi na kuri’u dubu 7,000 kuma a karshe mutanen suka ce “wannan mutumin ya kasance jakadan mu”.

Doguwa, wanda ke wakiltar mazabar Doguwa/Tudun ta tarayya, ya bayyana cewa ya yi iya kokarin sa kan nasarar jam’iyyar APC, inda ya jaddada cewa yanzu lokaci ya yi da za a saka masa da wannan matsayi.

“Na gane cewa ya zama dole na amsa kiran mutanen da suka yi imani da iyawa ta na neman mukamin shugaban majalisar wakilai,” in ji shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama mata da maza da ke aikata badala

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama mata hudu...

Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Magantu Kan Batun Sheikh Abduljabbar

Hukumar Gyaran Hali ta Jihar Kano ta bayyana cewa...

Dalilin da ya sa na bar tafiyar Kwankwasiyya – Farouk Lawan

Tsohon ɗan majalisar tarayya, Farouk Lawan, ya bayyana cewa...

An Dauke Shaikh Abduljabbar Daga Gidan Yari na Kurmawa Zuwa Wani Wuri – Yan uwansaba

Wani labari da ke yawo a kafafen sada zumunta...