Yaƙin Sudan: Dangote da MTN sun tallafawa yan Nigeria da aka dawo da su gida

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

Ministar ma’aikatar jin kai, Sadiya Umar-Farouq ta sanar da cewa gidauniyar Dangote ta bayar da tallafin N100,000 ga kowane daya daga cikin daliban wadanda suka dawo Sudan daga gidauniyar Dangote.

Da take jawabi yayin karbar kashin farko na ‘yan Najeriya 376 da suka makale a kasar Sudan da yaki ya daidaita a filin jirgin saman Abuja, Ministar ta kuma bayyana cewa gidauniyar MTN ita ma ta bayar da gudunmuwar data 25GB da katin waya na N25,000 ga kowane daya daga cikin wadanda suka dawo.

Da dumi-dumi: Allah kadai yasan jam’iyyar da zan mikawa mulkin Kano – Ganduje

A cewarta, tallafin Naira 100,000 da gidauniyar Dangote ta bayar, an baiwa wadanda aka dawo da su din ne domin su yi amfani da kudin wajen tafiya garuruwan su cikin sauki.

Shi ma da yake nasa jawabin jakadan Sudan a Najeriya Mohammad Yusuf yace nan bada jimawa ba za’a shawo kan lamarin Sudan.

Yusuf ya nuna farin cikinsa da yadda Najeriya ta samu nasarar kwashe ‘yan kasarta lami lafiya.

Jakadan wanda ya bayyana Sudan a matsayin kasa ta biyu ga ‘yan Najeriya da dama, ya ce nan ba da jimawa ba za a dawo da zaman lafiya a kasar da yaki ke neman daidaitawa.

Bizpoint ta rawaito Darakta Janar na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa, NEMA, Mustapha Ahmed, ya ce ana sa ran karin jirage guda hudu da ke jigilar ‘yan Najeriya daga Sudan zuwa Najeriya ranar Alhamis din nan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bai dace ɗalibai su rika murnar kammala karatu ta hanyoyin da ba su dace ba – Mal Ibrahim Khalil

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa ‎ ‎ ‎Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano...

Budaddiyar Wasika ga Gwamnan Kano kan wanda zai maye gurbin Muhuyi Magaji R/gado daga Kungiyar Lauyoyi yan Kano

Zuwa ga Mai Girma Alhaji Abba Kabir Yusuf Gwamnan Jihar Kano Gidan...

Dan majalisa Bichi ya sake biyan kuɗin makarantar dalibai 121 masu karatun digiri na biyu da na digirin digirgir

Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Mazabar Bichi a Majalisar...