Daga Sani Idris Maiwaya
Yayin da duniya ke bikin ranar ‘yancin ‘yan jarida, zababben Gwamnan Jihar Kano, Engr. Abba Kabir Yusuf, ya bukaci masu kafafen yada labarai da ‘yan jarida da su jajirce wajen bayar da sahihan labarai yayin da suke ci gaba da kare ‘yancin fadin albarkacin baki a cikin al’umma.
Engr. Abba ya ce idan aka samu sahihin rahotanni, kafafen yada labarai za su cigaba da tsare mutuncin su da matsayinsu na masu sa ido a al’amuran da suka shafi al’umma Kuma hakan shi zai basu damar dauke nauyin da aka dora musu.
Da dumi-dumi: Allah kadai yasan jam&l’iyyar da zan mikawa mulkin Kano – Ganduje
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da babban Sakataren yada labaran zaɓaɓɓen gwamnan kano Sunusi Bature Dawakin Tofa ya sanyawa hannu kuma aka aikowa kadaura24.
Zababben gwamnan ya yi kira ga dukkan bangarorin shugabanni da su bayar da gudunmawarsu wajen tabbatar da ‘yancin ‘yan jarida ta hanyar kare hakkin masu aikin yada labarai a duniya.
Engr. Abba Kabir ya ce gwamnatin jihar mai jiran gado za ta hada kai da kafafen yada labarai domin bunkasa rikon amana da shugabanci na gari ta hanyar bayar da bayanai na gaskiya .
Zababben Gwamnan, ya tabbatar wa da ‘yan jarida da al’ummar Kano, cewa a karkashin mulkin sa zai tabbatar da ‘yancin aikin jarida musamman idan ba a tauye mutunci da da’a da ke jagorantar sana’a mai daraja ba.