Daga Abubakar Sa’eed Sulaiman
Fitacciyar jarumar Shirin nan na tashar Arewa24 wato Dadin kowa Sarah Aloysius da akafi sani da Stephanie ta walaffa hoton ta da Nasir na Dadin Kowa a shafinta na Facebook.
Tun lokacin da ta wallafa hotunan mutane da dama suke ta bayyana albarkacin bakinsu kan batun, Kuma mutane da yawa suna ganin kamar akwai yiwuwar aure a tsakanin su.
Da dumi-dumi: Allah kadai yasan jam’iyyar da zan mikawa mulkin Kano – Ganduje
Ta wallafa a cikin harshen Turanci cewa abun da aka dade ana jira “Ina farin ciki da yin haka, nakuma kasance dakai har Abada aminina”.
Ciki harda wallafa wasu alamomi na Aure da soyayya kamar haka: 💍🔐💝👩❤️💋👨
Jaridar kadaura24 ta tuntubi jaruma Stephanie don jin takamaimai abun da take nufin aka wadancan hotuna data wallafa, amma bata daga wayar wakilin mu amma mun tura mata sakon kartakwana da zarar mun ji daga kareta zamu sanar da masu bibiyarmu.