Daga Maryam Ibrahim Zawaciki
Kamfanonin jiragen saman da aka zaɓa domin jigilar maniyata aikin hajjin bana a Najeriya sun ƙi yarda su sa hannu a kan yarjejeniya da Hukumar kula da aikin Hajji ta ƙasar saboda rikicin Sudan.
Tun farko an shirya kamfanonin za su rattaba hannu ne ranar Alhamis, amma yanzu an ɗage sai Talata mai zuwa, saboda wakilan kamfanonin sun nemi a ba su damar tattaunawa da shugabanninsu.
Me ke Shirin faruwa tsakanin Stephanie da Nasir Danmalan na Shirin Dadin kowa ?
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Wakilan kamfanonin jiragen sun haɗa da na Air peace da Azman Air da Max Air da kuma Aero Contractors.
Sai dai jirgi ɗaya da zai yi aikin na ƙasar waje shi ne Fly Nas kuma tuni ya rattaba hannu, inda a yarjejeniyar aka amince zai yi jigilar maniyyata 28,000 kimanin kashi 40% na mahajjatan bana daga Najeriya.
Da dumi-dumi: Allah kadai yasan jam’iyyar da zan mikawa mulkin Kano – Ganduje
Rufe sararin samaniyar Sudan saboda rikici, zai shafi jigilar aikin hajjin bana daga wasu ƙasashen Afirka, saboda ita ce hanya mafi gajartar zuwa kasar Saudiyya.
Idan aka sake sabuwar yarjejeniya tsakanin Hukumar NAHCON da masu kamfanonin jiragen sama, akwai yiwuwar kuɗaɗen aikin hajjin za su ƙaru, a kuma sake nazari kan tsare-tsaren aikin Hajjin.
A watan Afrilu ne NAHCON ta ƙayyade mafi ƙarancin kuɗin da za a biya na aikin hajji daga naira miliyan 2.88 zuwa naira miliyan 2.9.