Rashin kishin kano ne zai sa mutum ya rushe Ginin da mukai a tsohuwar Daula Otel – Ganduje

Date:

Daga Nasiba Rabi’u Yusuf

 

Gwamnan Jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa mara kishin jihar ne kadai zai iya hawa gireda har ya rushe sabon ginin kasuwar zamani da akai a tsohuwar Daula Otel dake birnin kano.

” Sama da shekaru 20 aka bar ginin na Daula Otel ba abun da ake a cikin sa , sai yara da aka bari suke shaye-shaye da Kuma barayi da suka Mayar da wurin wajen kwanan su da boye makamai, to meye laifin don mun yi wannan tsari da zai habbaka kasuwanci da tattalin arzikin jihar kano “.inji Ganduje

Ba wani ma’aikaci a Kano da yake bina ko sisin kobo – Ganduje ya bugi Kirji

Kadaura24 ta rawaito Gwamna Ganduje ya bayyana hakan ne lokacin da je niyar ganin yadda aikin ginin kasuwar zamani ta Daula Otel ke gudana..

Yace gwamnatin Kano ta shiga yarjejeniya da yankawasu ne akan wurin saboda inganta kasuwanci da kuma samar da kudaden shiga ga gwamnati, ” wannan tasa muka baiwa yan kasuwa su Gina da kudin su ita gwamnati dama filin ta ne sai aka samar da tsarin da kowa zai amfana.

Ganduje ya kara da cewa a yadda gwamnatin jihar kano take cibiyar kasuwancin Nigeria dole ne samar da tsari irin na zamani domin kanon ta cigaba da rike kambunta na cibiyar kasuwancin Nigeria.

 

Yadda Sabon ginin na Daula Otel yake kenan

” Mun yi yarjejeniya da kamfanin da ya yake aikin Kuma duk wasu al’amura na shari’a mun riga mun cika su, don haka maga wanda zai ce zai hau gireda yace zai rushe wannan gini” . A cewar Ganduje

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Wata sabuwa: Sanata Barau Jibrin ya gana da Baffa Bichi da Muhd Diggol

Tsohon sakataren gwamnatin Jihar Kano Dakta Abdullahi Baffa Bichi...

Rikicin Masarautar Kano: Kotu ta Sake Sabon Hukunci

A wani sabon yanayi na rikicin Masarautar Kano, Kotun...

Gidauniyar Aliko Dangote za ta rabawa ‘yan Najeriya miliyan daya shinkafa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Gidauniyar Aliko Dangote ta raba buhunan...

Rufe Makarantu da azumi: Ministan Ilimi ba ta da ilimin harkokin mulki – Jafar Sani Bello

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Tsohon dan takarar gwamnan jihar Kano...