Daga Kamal Yahaya Zakaria
Kasar Masar ta ce za ta amince a kwashe ɗaliban Najeriya da ke gujewa yakin da ake yi a Sudan ta ƙasarta ne kawai idan Najeriyar ta cika wasu tsauraran sharuɗɗa.
Najeriya dai na da ɗalibai sama da 500 waɗanda suka maƙale a bakin iyakar ƙasar ta Masar, suna jiran izinin shiga domin kwashe su zuwa gida.
Jakadan Najeriya a Masar, Nura Abba Rimi ne ya tabbatar wa BBC da wannan bayanin.
Masarautun kano 5 nan gani nan bari – Gwamna Ganduje
A baya ƙasar Habasha ta hana ɗaliban Najeriya bi ta ƙasarta domin tsere wa faɗan na Sudan, wani abu da ya janyo suka daga ɓangarori da dama.
Ambasada Nura Abba Rimi ya ce sharuɗɗan da ƙasar ta Masar ta gindaya su ne:
Ranar Ma’aikata: Zamu inganta rayuwar ma’aikatan gwamnati, ta Biyan Albashi da Fansho cikin gaggawa – Abba Gida-gida
Dole sai Najeriya ta bayyana tsarin da ta yi na jiragen da za su sauka a ƙasar domin kwashe ɗaliban.
Girman jiragen saman da za su yi jigilar.
Tabbatar da cewa za a zarce da ɗaliban kai-tsaye daga bakin iyakar ƙasar zuwa filin jirgi da aka yarje
Cikakken jerin sunayen mutanen da za a kwashe ta ƙasar da kuma lambar fasfo ɗinsu na tafiye-tafiye.
Cikakkun takardun tafiya.
Kasancewar jami’an gwamnatin Najeriya a wuraren kwashe ɗaliban.
Da kuma motocin safa da za su kwashi ɗaliban daga bakin iyaka zuwa filin jiragen sama.
ƙasashen duniya dai na ci gaba da rige-rigen ganin sun kwashe ƴan ƙasarsu daga Sudan, bayan ɓallewar faɗa tsakanin dakaru masu mubaya’a ga manyan hafsoshin sojin ƙasar biyu.