Masarautun kano 5 nan gani nan bari – Gwamna Ganduje

Date:

Daga Safiyanu Dantala Jobawa

Gwamnan Jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa Masarautu kano guda biyar da ya ƙirƙiro sun zo kenan sai mahadi ka Ture.
Kadaura24 ta rawaito ana ta rade-radin sabon zaɓaɓɓen gwamnan kano Engr. Abba Kabir Yusuf zai rushe Masarautu da zarar an rantsar da shi a matsayin gwamnan Kano a ranar 29 ga watan mayu.
Gwamna Ganduje ya bayyana hakan ne yayin jawabinsa na ranar bikin ma’aikata ta bana, wanda aka gudanar a filin wasa na Sani Abacha dake kano.
” Mun ƙirƙiro Masarautun nan guda biyar don inganta tsaro, don samar da cigaba, inganta tarihi da samar da kananan burane a kano”. Inji Ganduje
Ganduje ya kara da cewa babu wanda zai rushe wadancan masarautu, sun zama mahadi ka ture Kuma ko mahadin da zai rushe Masarautun ma Allah ba zai kawo shi ba da yardar Allah “.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama mata da maza da ke aikata badala

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama mata hudu...

Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Magantu Kan Batun Sheikh Abduljabbar

Hukumar Gyaran Hali ta Jihar Kano ta bayyana cewa...

Dalilin da ya sa na bar tafiyar Kwankwasiyya – Farouk Lawan

Tsohon ɗan majalisar tarayya, Farouk Lawan, ya bayyana cewa...

An Dauke Shaikh Abduljabbar Daga Gidan Yari na Kurmawa Zuwa Wani Wuri – Yan uwansaba

Wani labari da ke yawo a kafafen sada zumunta...