Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa, NDLEA, ta gano wani waje a jihar Adamawa da ake aikin haɗa abun saka maye mai suna akuskura a ke kuma kai wa kasashen Chadi da Kamaru da Jamhuriyar Nijar.
“A lokacin da aka kai farmakin, jami’an mu na NDLEA sun tarar ana ci gaba da gudanar da ayyukan haɗa ƙwayar ” in ji shi, ya kara da cewa an kama ƙwayoyi masu yawa”.
Ƙasar Saudiyya ta gindaya sharuɗɗan fita da Zamzam daga ƙasar
Mai magana da yawun hukumar, Femi Babafemi ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a yau Lahadi a Abuja, inda ya ce jami’an hukumar ne suka kai samame wajen a jiya Asabar a garin Mubi.
Da dumi-dumi: Kwankwaso ya Magantu a kan batun dawo da Sarki Sunusi II Sarautar Kano
A ɗaya ɓangaren kuma ya ce jami’an hukumar Benue sun kwato kwalaben Syrup na Codeine guda 859 wanda nauyinsu ya kai kilogiram 117.3 da wani da ake zargin dila ya zubar da su.
Mai magana da yawun hukumar ta NDLEA ya ce an zubar da kwalaben maganin tarin ne daga nisan kilomita biyu daga shingen binciken hukumar NDLEA da ke kan hanyar Enugu zuwa Otukpo a ranar Laraba.
Babafemi ya kuma ce an kama wasu mutane biyu Kabiru Muhammed mai shekaru 35 da kuma Isah Muhammed mai shekaru 28 dauke da buhun tabar wiwi 20 mai nauyin kilogiram 11.2 da aka boye a cikin buhun rogo (garri) a kan hanyar Zaria zuwa Kano ranar Juma’a.