Hukumomin filin jirgin sama na Sarki Abdulaziz da ke birnin Jidda na kasar Saudiyya sun sanya sharuda guda hudu ga duk wanda ya yi ziyara yake so ya tafi ƙasarsa da ruwan Zamzam.
Cikin wata sanarwa da aka fitar game da masu ibadar da za su koma ƙasashensu da ruwan zamzam, an haramtawa masu ɗaukar robar ruwan Zamzam a cikin kayansu, sai dai su riƙe shi a hannu a cikin jirgi.
Da dumi-dumi: Kwankwaso ya Magantu a kan batun dawo da Sarki Sunusi II Sarautar Kano
Masu gudanar da ayyukan sun sanar da cewa ko wanene ke son siyan Zamzam sai dai ya siya daga ainihin waɗanda ke siyarwa a wuraren tsayawarsu, kuma lita biyar kawai aka yarda mutum ya ɗauka.
Ko wanne mai ibada ba zai ɗauki sama da roba guda ba ta ruwan Zamzam, kuma sai ya nuna shaidar rijistar umara ta manhajar Nusuk.