Daga Halima Musa Sabaru
Rundunar ƴan sanda Kano, ta kama bindigogi kirar AK-47 guda hudu a kokarin yin fasakwaurinsu zuwa Kano.
A ranar juma’a ne ’yan sanda a yayin da suke sintiri a kwanar Garko da ke kan hanyar Kano zuwa Bauchi suka gano bindigogin a cikin wata motar bas kirar Hiace.
Da dumi-dumi: Kwankwaso ya Magantu a kan batun dawo da Sarki Sunusi II Sarautar Kano
Wadanda ake zargin sun hango motar ’yan sanda ne akan titi, sai motar ta fara kokarin juyawa, inda daya daga cikin mutanen motar ya fito ya jefar da kunshin abun dake cikin buhu, suka ja motar suka tsere.
Jam’iyyar NNPP ta zargi Ganduje da yin zagon kasa ga yunkurin sauyin gwamnati a Kano
Daga baya da ’yan sandan suka duba buhun sai suka ga bindigogi kirar AK-47 guda hudu a ciki.
Da yake sanar da faruwar lamarin, kakakin ’yan sandan jihar kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce rundunarsu tana ci gaba da bincike domin kamo mutanen da suka tsere.
Ya kuma bukaci al’umma da su kai rahoton duk wani wanda ba su aminta da motsinsa ba ga ofishin ’yan sanda mafi kusa da su.