Da dumi-dumi: Kwankwaso ya Magantu a kan batun dawo da Sarki Sunusi II Sarautar Kano

Date:

Daga Sani Idris Maiwaya

 

Jagoran Jam’iyyar NNPP na kasa Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, yace yanzu yayi wuri a fara batun cire sarki ko dawo da Wani Sarkin koma batun sauran masarautu da gwamnatin Ganduje ta samar.

 

” Yanzu dai Abba shi ne gwamnan kano, kuma nayi imanin zai zauna ya yiwa wannan batun duba na tsanaki , sannan Ina da yaƙinin Allah zai bashi damar warware wannan matun dama sauran matsaloli da zai samu idan an rantsar da shi”. Kwankwaso

Jam’iyyar NNPP ta zargi Ganduje da yin zagon kasa ga yunkurin sauyin gwamnati a Kano

Engr. Kwankwaso ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da yayi da manema labarai a kasar Kamaru.

” A wajen kamfe din mu, abun da muka nunawa mutane shi ne duk aiyukan alkhairin da muka faro lokacin muna gwamnati, shi wanann gwamna da mukarraban sa zasu dora daga inda muka tsaya, Kuma mu a matsayin mu na dattawa na tafiyar Insha Allah zamu rika bada shawarwari ta yadda zasu yi abun da ya dace”. Inji Kwankwaso

 

” Mun yi kokari bamu shigar da maganar ko za’a cire Sarki ko za’a yi kaza ba cikin yakin neman zaben mu, amma yanzu dama ta samu su wadanda Allah ya baiwa wanann ragama su zasu zauna mai daki shi yasan inda yake yi masa yoyo, zasu je su duba suga me ya kamata su yi a halin da suka sami kansu banda ma wannan akwai maganar sauran sarakuna da aka yi to kaga dole sai an yi nazari”.

 

Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito tun bayan bayyana Abba Gida-gida a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan Kano ake ta rade-radin za’a cire Sarkin kano a dawo da tsohon Sarkin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama mata da maza da ke aikata badala

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama mata hudu...

Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Magantu Kan Batun Sheikh Abduljabbar

Hukumar Gyaran Hali ta Jihar Kano ta bayyana cewa...

Dalilin da ya sa na bar tafiyar Kwankwasiyya – Farouk Lawan

Tsohon ɗan majalisar tarayya, Farouk Lawan, ya bayyana cewa...

An Dauke Shaikh Abduljabbar Daga Gidan Yari na Kurmawa Zuwa Wani Wuri – Yan uwansaba

Wani labari da ke yawo a kafafen sada zumunta...