Buhari ya amince da dage Kidayar 2023

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

 

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da dage kidayar jama’a da gidaje ta shekarar 2023 da aka shirya gudanarwa tun daga ranar 3 ga watan Mayu zuwa 7 ga watan Mayu.

Ministan yada labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed, ya bayyana hakan a ranar Asabar a Abuja, inda ya ce an dage aikin kidayar zuwa ranar da gwamnati mai jiran gado ta ayyana.

Da dumi-dumi: Kwankwaso ya Magantu a kan batun dawo da Sarki Sunusi II Sarautar Kano

 

A cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu da kan sa, ministan ya ce shugaban kasar ya amince da dage kidayar ne bayan ganawa da wasu mambobin majalisar zartarwa ta tarayya da shugaban hukumar kidaya ta kasa da yan tawagarsa.

 

Ministan wanda ke rike da mukamin Shugaban Kwamitin yawar da kan al’umma na Kasa kan Kidayar 2023, ya ce an gudanar da taron ne a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja a ranar Juma’a.

 

“A lokacin da aka yanke wannan matakin na dage kidayar, taron ya sake nanata muhimmancin gudanar da kidayar jama’a da gidaje, inda yace kimanin shekaru 17 kenan ba a gudanar da kidayar ba a Nigeria.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama mata da maza da ke aikata badala

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama mata hudu...

Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Magantu Kan Batun Sheikh Abduljabbar

Hukumar Gyaran Hali ta Jihar Kano ta bayyana cewa...

Dalilin da ya sa na bar tafiyar Kwankwasiyya – Farouk Lawan

Tsohon ɗan majalisar tarayya, Farouk Lawan, ya bayyana cewa...

An Dauke Shaikh Abduljabbar Daga Gidan Yari na Kurmawa Zuwa Wani Wuri – Yan uwansaba

Wani labari da ke yawo a kafafen sada zumunta...