A shirye muke mu mika mulkin kano ba tare da wata matsala ba – Ganduje

Date:

Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa

 

Gwamnatin jihar Kano ta ce a shirye take ta miƙa mulki ga sabuwar gwamnati cikin ruwan sanyi ba tare da wata matsala ba.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai Muhammad Garba ya sanyawa hannu kuma aka rabawa manema labarai a kano.

 

Gwamnatin ta ce tuni aka samar da babban kwamiti da kuma ƙananan da za su taimaka domin ganin an miƙa mulkin salin alin.

Da dumi-dumi: Kwankwaso ya Magantu a kan batun dawo da Sarki Sunusi II Sarautar Kano

Ya musanta iƙirarin kwamitin karɓar mulki na jam’iyyar NNPP na cewa gwamnatin Ganduje na yi wa shirin miƙa mulkin zagon ƙasa sakamakon rashin basu hadin kan da ya dace.

 

“Kwamitin miƙa mulki na ɓangaren gwamnatin Ganduje na rubuta rahoton ƙarshe kafin miƙa mulki. Ya bayyana cewa kamata ya yi kwamitin karɓa na gwamnati mai jiran gado shi ma ya shirya domin karɓar rahoton, wanda ya yi alƙawarin miƙawa a kan lokaci”. Inji Muhammad Garba

Jam’iyyar NNPP ta zargi Ganduje da yin zagon kasa ga yunkurin sauyin gwamnati a Kano

Kwamishinan ya ƙara da cewa manufar miƙa mulki shi ne gwamnati mai barin gado ta miƙa duk wasu abubuwa na tafiyar da shugabanci cikin ruwan sanyi. Ba yunkurin yaɗa wani tunani ko wata aƙida ba.

Ya kuma ce kamata ya yi gwamnati mai jiran gado ta mayar da hankali game da shirin da take yi na karɓar mulki, ta kuma kiyaye duk wani abu da zai iya janyo fitina a yayin miƙawar.

Ƙorafin da NNPP ta yi a jiya shi ne gwamnatin ta ba ta gurbi uku kawai a cikin kwamitin da aka kafa don miƙa mulki hannun sabuwar gwamnati.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin gida: Jam’iyyar APC ta Fara Tuhumar Kakakinta na Kano Ahmad S Aruwa

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jam'iyyar APC ta Mazabar Daurawa a...

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...