Daga Safiyanu Dantala Jobawa
Zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya kammala shirin naɗa tsohon gwamnan Akwa Ibom, Sanata Godswill Akpabio a matsayin shugaban majalisar dattawa, da kuma Sanata Barau Jibrin a matsayin mataimakin sa.
Sahihan majiyoyi sun bayyana wa jaridar Daily Trust cewa tuni Tinubu ya sanar da Akpabio da Barau wannan ƙuduri nasa a wata ganawar sirri da su ka yi a Abuja bayan dawowarsa daga ƙasar Faransa.
Yakin Sudan: Rukunin farkon na daliban Najeriya sun Isa Ƙasar Masar – Gwamnatin tarayya
Kadaura24 ta rawaito cewa Akpabio da Barau na cikin ƴan takara 9 da ke neman shugabancin majalisar dattawa, wanda za a rantsar da su a ranar 13 ga watan Yuni.
Majiyoyin sun tabbatar wa da Daily Trust cewa a yayin ganawar, wacce dama sabo da Barau a ka yi ta, Tinubu ya rarrashe shi da ya hakura da takarar shugabancin majalisar dattawa domin a samu adalci da daidaito na addini a shugabancin ƙasar.
Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya halarci Faretin Sojoji Sanye da kakin Soji
A cewar majiyoyin, Tinubu ya nunawa Barau cewa ya cancanta da ya zama shugaban majalisar dattawa, to amma kasancewar Tinubu da mataimakin sa Kasim Shettima musulmai ne, ya kamata a ce Barau ya ajiye burin nasa ya baiwa kirista dan kudu dama domin a samu daidaito da kuma zaman lafiya a mulkin ƙasar.
“A ƙarshen ganawar ne sai Tinubu ya shaidawa Barau cewa yana don ya zama mataimaki ga Akpabio su yi aiki tare,” in ji majiyoyin.