Daga Ibrahim Sani Gama
Jam’iyyar NNPP ta zargi gwamnatin jihar Kano da yin zagon kasa ga shirin karbar mulki da sabuwar gwamnati dake yi a jihar.
Kadaura24 ta rawaito a zantawarsa da manema labarai,Dr. Abdullahi Baffa Bichi, shugaban kwamitin karɓar mulki na zaɓaɓɓen gwamnan NNPP, ya bayyana cewa da gangan gwamnatin Abdullahi Ganduje ta ke kokarin kawo tsaiko ga kwamitin karɓar mulki, inda ta ware wa jam’iyyar NNPP kujeru uku kacal a cikin kwamitin da suka gabatar na mika mulki.
“Muna kallon wannan a matsayin wani yunƙuri ne da gangan na kawo tsaiko ga karbar mulki ga sabuwar gwamnati a jihar, kuma a’ummar jihar kano babu abin da suke tsammata sai samun sauyin gwamnatin cikin kwanciyar hankali da lumana.” inji Bichi
Shugabancin majalisa: Abubuwan da aka tattauna tsakanin Tinubu, Akpabio da Barau Jibri
A cewar Bichi, gwamnatin mai barin gado ta bukaci su bayar da sunayen mutane uku da za su shiga cikin kwamitin gwamnatin, lamarin da suke ganin hakan bai dace ba.
Bichi ya kara da cewa, babban abin da ake ta cece-kuce a kai shi ne ka’ida, kasancewar ba ‘yan jam’iyya daya ba ne, kuma ba su da manufa daya da dabi’u iri daya.
“Sauyin gwamnati iri uku ne, akwai wanda gwamna yake gadar kansa ta hanyar zarcewa, da kuma sauyin gwamnatin na jam’iyyar siyasa daya, da kuma sauyin gwamnati daga wata jam’iyyar zuwa wata jam’iyyar”. Inji Baffa Bichi
“A wannan matsayin mu muna matsayin mu wadanda suke jam’iyyar daban da ta gwamnati mai barin gado, don haka ya kamata su sanda da cewa manufar mu daban da tasu, jam’iyyar mu daban da sauran bambamce-banbance”. Bichi
Sai dai shugaban kwamitin karɓar mulkin jam’iyyar NNPP ya bayyana shirin su na yin hulda da manyan sakatarorin gwamnati da daraktoci domin tabbatar da mika mulki ga gwamnati ba tare da wata matsala ba.
Ya yi kira ga Gwamna Ganduje da ya ba da hadin kai tare da tabbatar da mika mulki cikin sauki.
“Muna kira ga Gwamna Ganduje da ya sanya maslahar al’ummar Jihar Kano a gaba, ya kuma hada kai da mu wajen ganin an samu sauyin gwamnatin ba tare da wata matsala ba.
“Mun kuduri aniyar yin aiki don ganin an mika mulki cikin sauki, kuma muna fatan gwamnatin mai barin gado za ta yi hakan,” in ji Bichi.