Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Shugaba Buhari ya halarci faretin ƙaddamar da sabbin launuka na rundunonin sojin Najeriya a birnin Abuja.
Buhari wanda ya isa dandalin Eagle Square, inda aka gudanar da faretin, da misalin karfe 10:18 na safe ya samu rakiyar shugaban ma’aikatan fadar sa Farfesa Ibrahim Gambari.
Yakin Sudan: An kaiwa daliban Nigeria hari
Buhari wanda tsohon Janar diin soja ne ya Isa wurin faretin sanye da kakin soji na bikin kuma ya duba sojoji sama da 1,000 wadanda suka gudanar da faretin.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa babban hafsan hafsoshin tsaron Najeriya Janar Lucky Irabor, babban hafsan sojin kasa, Laftanar-Gen. Faruk Yahaya, da Sufeto-Janar na ‘yan sanda Usman Baba ne suka halarci taron.
Shugaban hafsan sojin sama, Air Marshal Oladayo Amao; Babban Hafsan Sojin Ruwa, Rear Admiral Awwal Zubairu Gambo, Shugaban Majalisar Dattawa Ahmad Lawan na daga cikin manyan bakin da suka halarci taron.