Yakin Sudan: An kaiwa daliban Nigeria hari

Date:

Daga Hanifa Ahmad

 

Wasu ‘ƴan daba sun kai hari kan wasu daliban Nijeriya a hanyarsu ta komawa masaukinsu, da ke wajen birnin Khartoum na kasar Sudan.

 

Wani ganau da ya tsallake rijiya da baya, Idris Bello, ya shaidawa DAILY NIGERIAN ta wayar tarho cewa lamarin ya faru ne a kusa da titin Napasha da misalin karfe 7 na yammacin jiya Laraba.

Zargin kisan kai: Ba da gangan aka jinkirta shari’ar Alhassan Ado Doguwa ba – Gwamnatin Kano

A kara da cewa, biyar daga cikin daliban sun tsallake rijiya da baya, amma wani dalibi mai suna Umar Hudu, ɗan shekara 21 ya samu munanan raunuka.

Hukumar Yan Sanda ta turo sabon kwamishinanta kano

“Mu kan taru tun safe har yamma a Jami’ar kasa da kasa ta Afirka a ci gaba da kwashe mu da gwamnatin Nijeriya ta fara. Wasu daga cikin mu da ba su yi sa’a an kwashe su ba a yau, sai su ka koma masaukin su kafin su dawo wurin washegari.

A kan hanyarmu ta komawa gida, sai wasu gungun ƴan daba su ka tare mu su ka kai mana hari da muggan makamai.

“Mu biyar daga cikinmu mun tsira ba tare da samun rauni ba amma daya a cikin mu, Hudu Umar ya samu munanan raunuka. Jini ya zuba a jikinsa sosai dan babu asibitin da za’a kaishi.

“Na yi amfani da ɗan ƙaramin ilimina a matsayina na ɗalibin likitanci na duba shi na samu na tsayar masa da jinin da ke ta zuba, ” in ji shi.

Jaridar kadaura24 ta rawaito cewa a jiya Laraba ne Nijeriya ta fara aikin kwashe ‘yan ƙasar da su ka makale a Sudan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kotu a Kano ta hukunta masu shago saboda zubar da shara a kan titi

Kotun tafi da gidanka da ke Kano ta yanke...

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama mata da maza da ke aikata badala

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama mata hudu...

Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Magantu Kan Batun Sheikh Abduljabbar

Hukumar Gyaran Hali ta Jihar Kano ta bayyana cewa...

Dalilin da ya sa na bar tafiyar Kwankwasiyya – Farouk Lawan

Tsohon ɗan majalisar tarayya, Farouk Lawan, ya bayyana cewa...