Daga Rahama Umar Kwaru
A Yau Litinin ne ake sa ran zaɓaɓɓen shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu zai dawo gida Nigeria.
Tinubu zai koma Najeriya ne bayan ya shafe tsawon mako biyar a Paris, inda ya huta, bayan kammala yaƙin neman zaɓen da ya ba shi nasara.
Kifewar kwale-kwale ta yi sanadiyyar Rasuwar Mutane 5 a Kano
Tun farko an tsara cewa zaɓaɓɓen shugaban na Najeriya zai kwan biyu a Paris cikin ƙasar Faransa, daga nan kuma ya wuce zuwa birnin London, kafin ya dangana da ƙasar Saudiyya.
Sai dai rashin ganin sa a ƙasar Saudiyya lokacin aikin umra, musamman daidai lokacin da shugaban ƙasar mai barin gado, Muhammadu Buhari yake can, ya haifar da jita-jita da raɗe-raɗi.
Wani mataimakinsa na musamman Bayo Onanuga ne ya tabbatar da rahoton komawar Tinubun Najeriya, ko da yake bai cewa ga taƙamaimai lokacin da zai sauka a ƙasar ba.