Kifewar kwale-kwale ta yi sanadiyyar Rasuwar Mutane 5 a Kano

Date:

Daga Aisha Aliyu Umar

 

Hukumar kashe gobara ta jihar Kano a ranar Lahadin da ta gabata ta tabbatar da mutuwar mutane biyar yayin da wasu shida suka tsira daga hatsarin kwale-kwale a Dam Kanwa da ke karamar hukumar Madobi .

 

Kakakin hukumar, Saminu Abdullahi, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Najeriya a wata tattaunawa ta wayar tarho yace wani Umar Faruk-Dalada, ne ya sanar da su labarin halin da ake ciki da kuma inda ya faru.

Hutuna: Yadda Sarkin Kano ya gudanar da Hawan Nasarawa

Ya ce: “Lamarin ya faru ne a ranar 22 ga Afrilu, da misalin karfe 05:40 na yamma.

 

“Akwai mutane 11 a cikin kwale-kwalen, an ceto shida yayin da guda biyar kuma suka rasa rayukansu.

Sunayen wadanda suka rasa rayukansu a hatsarin sun hada da Abdulrazak Nabara mai shekaru 40; Dalha Muktar-Atamma, 40; Mustapha Ibrahim, 45; Umar Isah mai shekaru 35 da Umar Idris mai shekaru 35,” inji shi.

ya ce wadanda abin ya shafa sun fito ne daga karamar hukumar Fagge ta jihar kano.

Ya ce an fara gudanar da bincike kan hatsarin kwale-kwalen kuma za a sanar da musabbabin faruwar lamarin da zarar an kammala bincike.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Abubakar Bichi ya bada gudumawar motocin bas 13 ga jami’o’in Kano da taraktoci 11 ga yan mazabarsa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu Dan Majalisar tarayya mai wakiltar karamar...

Rikicin Sarautar Kano: Fadar Sarki Sanusi ta zargi magoya bayan Sarki Aminu Ado Bayero da kai farmaki Kofar Kudu

Daga Sani Idris Maiwaya   Rikicin Masarautar kano ya na neman...

Shugabannin Kasuwar Kanti Kwari sun shiryawa Gwamnan Kano Addu’o’i na musamman

Daga jafar adam Shugaban kasuwar Kantin Kwari Sharu Abdullahi Namalam...