Daga Com. Umar Hamisu K/Na’isa
Mai martaba sarkin Gaya Alh (Dr) Aliyu Ibrahim CNA, NIM, CPA (kirmau Mai gabas), ya Gudanar da Hawan Bagauda a safiyar yau lahadi inda yabi ta rindin Giginya zuwa Bagauda. Daga bisani yaje sakatariyar karamar Hukumar Gaya domin Gaisawa da shugabannin kana Nan hukumomin mu Guda Tara(9) da sauran daukacin Al’umma.
A zamanin Mai martaba sarkin Gaya Dr. Aliyu Ibrahim aka kirkiro Hawan Bagauda domin farfado da Tarihi.