SSS sun kama wasu ‘yan bindiga 2 a Kano

Date:

Daga Rahama Umar Kwaru

 

Hukumar tsaron farin kaya, ta SSS ta kama wasu ‘yan bindiga guda biyu a Kano dauke da bindigu kirar AK-47 guda 2 da kuma mazubin harsashi na AK-47 da babu komai a ciki.

 

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar ta SSS na ƙasa, Peter Afunanya ya fitar, ya ce wadanda aka kama din na shirin wucewa ne domin kai makaman inda su ka shirya kai hari a daya daga cikin Jihohin Arewacin Nijeriya.

Gawuna ya yi wa Musulmi Barka da Sallah, Ya Bukaci su yiwa kasa Addu’ar Zaman Lafiya

Ya ce rundunar ta kuma kwace babur kirar boxer da kuma buhun doya da su ka boye bindigun a ciki.

Abba Gida-gida ya Gargaɗi al’umma game da tukin ganganci, yayin bukukuwan Sallah

“Wannan ci gaban ya nuna bukatar al’umma su kasance cikin taka-tsan-tsan tare da kai rahoton duk wani motsi, mutane ko wani abu da ba a yarda da shi ba zuwa ga jami’an tsaro da ke kusa da su.

“An umurci masu gidajen shaƙatawa, baƙi da cibiyoyin yawon buɗe ido da su yi taka-tsan-tsan a lokacin bukukuwan Sallah. Kamata ya yi su kara daukar matakan tabbatar da tsaron wuraren su.

“Bayan haka, hukumar na yi wa Musulmi masu aminci da zaman lafiya murnar bukukuwan Eid al-Fitr. Hukumar mu ta yi alkawarin yin aiki tare da sauran hukumomin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki don samar da isasshen tsaro a lokacin da kuma bayan Sallah,” in ji Mista Afunanya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta sake maka Ganduje da ya’yansa a gaban Kotu

Gwamnatin jihar Kano ta kai tsohon gwamnan jihar, Dr....

Kungiyar Ma’aikatan Jinya da Ungozoma ta koka da kalaman mataimakin gwamnan Kano

Kungiyar Ma’aikatan Jinya da Ungozoma ta Najeriya (NANNM) reshen...

Kotu a Kano ta hukunta masu shago saboda zubar da shara a kan titi

Kotun tafi da gidanka da ke Kano ta yanke...

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama mata da maza da ke aikata badala

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama mata hudu...