Daga Maryam Ibrahim Muhammad
Wani Malamin addinin musulunci a Kano Mai suna Malam Muhammad Dauda Lokon makera ya gargadi al’umma da su guji komawa sabon Allah bayan kammala azumin watan Ramadana.
” Ramadana makaranta ce da ake son kowa yayi koyi da abubun alkhairin da ya koya, musamman a wuraren Tafsirin Al’qur’ani da sauran wuraren karatuttuka don cigaba da samun yardar Allah S W A”.
Gawuna ya yi wa Musulmi Barka da Sallah, Ya Bukaci su yiwa kasa Addu’ar Zaman Lafiya
Malam Dauda Lokon makera ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da yayi da jaridar kadaura24 a Kano.
Abba Gida-gida ya Gargaɗi al’umma game da tukin ganganci, yayin bukukuwan Sallah
Yace an so mutane su cigaba da kasance a yadda suke a watan Ramadana, musamman ta wajen gujewa sabon Allah da kuma taimakawa masu karamin karfi.
” Kyauta da sadakar da aka rika yi a watan Ramadana kamata yayi mutane su cigaba, babu shakka idan suka cigaba hakan zai taimaka wajen rage talauci da kuma rage gaba tsakanin mawadata da mabukata “. Inji Malam Dauda Lokon makera
Malam Dauda ya yi fatan mawadata zasu dore da yalwatawa marayu da masu karamin karfi a kowanne lokaci don kyautata zamantakewa da kuma neman yardar Allah (S W A).