Teloli a Kano sun bayyana dalilan da yasa mutane da yawa ba zasu sami dinkin Sallah ba

Date:

 

Mutane da dama na kasancewa cikin bacin rai, da damuwa sakamakon yadda suke rasa dinkin Sallah, saboda karatowar bukukuwan Sallah a jihar Kano .

Jihar Kano dai, daular Musulunci, da ta yi fice a bikin Sallah mafi kyau a duniya, bisa la’akari da tarihinta na addini da kuma dimbin al’adun mutanen jihar.

 

A duk lokacin bukukuwan Sallah, musamman ma na karamar Sallah suka zo, kasuwannin masaku da kayan kwalliya na cika makil da mutane, sannan masu sana’ar dinki na cin kasuwar su a lokacin sakamakon yawan mutanen da suke yin dinki a lokacin.

Falakin Shinkafi ya rabawa Marayu 100 kayan Sallah a Kano

Sai dai masu sana’ar dinki a jihar kano suna sanya mutane da yawa cikin wani yanayi mara dadi sakamakon rashin yi musu dinkinsu na Sallah akan lokaci, a bana ma dai akwai yiwuwar samun irin wannan matsalar a wurare daban-daban a jihar kano da saura sauran jihohin Musulmi.

 

Wasu masu sana’ar dinki da suka zanta da jaridar BizPoint a karamar hukumar Fagge, yankin da aka fi samun madunka a jihar kano, sun ce yawancin kwastomominsu ba sa kawo kayan dinkin nasu kafin ko farkon watan Ramadan.

Fatawa: Ya halatta ayi zakkar fidda kai da Taliya Kuskus ko Indomie – Mal Ibrahim Khalil

A cewarsu, galibinsu suna kwana a shagunansu ne saboda ba su da wani aiki da yawa da za su yi a farkon watan Ramadan saboda kwastomomin ba su fara kawo dunkunasu na Sallah ba.

Wani shahararren tela a yankin, Mai suna Salisu Barack, wanda aka fi sani da Salisu Aljan, ya ce da yawa daga cikin kwastomominsa ba sa shirya kawai kayan su kafin Sallah.

Da yake ba da dalilansa, Aljan ya ce saboda matsalar rashin kudi, yawancin abokan cinikin su, suna kasa samun kudin siyan kayan a farkon watan Ramadan.

A cewarsa, ana tsakiyar watan Ramadan na bana ne kwastomomin bayan sun fara samun kudade, shi ne suka fara tururu zuwa shagunan dinki don kai dinkin kayansu na Sallah.

“Kamar yadda nake magana da ku a yanzu, ba zan iya bayyana yadda zan kammala aiyukan da aka kawo min kafin Sallah ba. Aikin da ke gabana babba ne wanda ba zan iya kammala shi kafin Sallah ba.

Wani tela mai suna Ibrahim Blacky ya ce yana kwana a shagon ne a kokarinsa na ganin ya samu nasarar kammala aiyukan dake gaban sa, kafin Sallah.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Wata sabuwa: Sanata Barau Jibrin ya gana da Baffa Bichi da Muhd Diggol

Tsohon sakataren gwamnatin Jihar Kano Dakta Abdullahi Baffa Bichi...

Rikicin Masarautar Kano: Kotu ta Sake Sabon Hukunci

A wani sabon yanayi na rikicin Masarautar Kano, Kotun...

Gidauniyar Aliko Dangote za ta rabawa ‘yan Najeriya miliyan daya shinkafa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Gidauniyar Aliko Dangote ta raba buhunan...

Rufe Makarantu da azumi: Ministan Ilimi ba ta da ilimin harkokin mulki – Jafar Sani Bello

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Tsohon dan takarar gwamnan jihar Kano...