Daga Ibrahim Sani Gama
An shawarci kungiyoyi masu zaman kansu da mawadata, da su kara zage damtse wajen tallafawa marayu da marasa karfi a cikin Alumma domin rage wahalhalu da fatara ta wannan zamanin.
Shahararren malamin nan sheikh Malam Ibrahim Khalili ne ya ba da shawarar bayan kammala shan ruwa wanda Gidauniyar tallafawa marayu ta (C AND C) ta shirya a Mumbayya House dake jihar kano.
Malam Ibrahim Khalili, yace yana da muhimmanci da kyautatawa irin wadannan kungiyayo da ɗai-ɗaikun mutane musamman masu hannu shuni su rika shirya bude baki don taimakawa marayu da marasa hali.
Gwamna Ganduje ya nada Surajo Umar Wudil a matsayin SSA
Malam Khalili ya jadadda cewa rashin aiwatar da tallafi irin wadannan, ya sanya al’umma suka tsinci kansu a ciki talauci da kin juna da gurbacewar marayun da
aka mutu aka barsu, sakamakon watsi da aka yi da su.
Fatawa: Ya halatta ayi zakkar fidda kai da Taliya Kuskus ko Indomie – Mal Ibrahim Khalil
“Akwai bukatar kungiyoyi su yi amfani da wannan dama da yin koyi da Gidauniyar nan, wajen hada kawunansu da sanyawa kansu harajin da za su rika taimakawa marayu da zawarawa da kananan yara da aka mutu aka barsu, duba da Falalar dake cikin baiwa marayu taimako, musamman a lokacin da suke da bukatar haka”.inji shi
Malam Ibrahim Khalili, ya kuma bukaci yanjaridu da sauran kafafen yada labarai, da su taimakawa wannan Gidauniya wajen yada manufarta da ayyukan da take yi domin karawa sauran al’umma karsahi da kwarin gwiwa na aiwatar da aiyukan alkhairi .
A jawabinsa shugaban Gidauniyar na kasa Sunusi Garba Kalamaina,ya bayyana cewa, sun kafa Gidauniyar ne, domin taimakawa marayu da marasa hali wajen biya musu kudaden magani da raba musu Abinci da daukar Nauyin karatun marayu, a cikin jihohin Arewacin Najeriya.
Sunusi Garba yace duk wadannan tallafe_tallafe da kungiyar take yi, tana yi ne da karfinta da dukiyarta ta hanyar tattara taimakon kudade da kayayyakin amfani da al’umma ke bukata domin ganin marayu su ma sun ji dadin aiwatar da rayuwarsu kamar sauran al’umma da ba marayu ba.
Shugaban Gidauniyar yace ko kwanan nan, Gidauniyar ta je gidajen marayu, Wanda ta samu damar tallafawa marayu da kayayyaki da abubuwan bukata na kudade da dama.
“Gidauniyar tana zuwa Gidajen rediyo da Asibitoci domin daukewa masu bukatar taimako,Wanda wasu lokutan ma zaka ga kudin maganin da wani ko wata za su biya na magunguna ba ya wuce naira Dubu biyu ko biyar, amma sakamakon bashi,dashi babu yadda zai yi”. A cewar Sanusi Garba
Sunusi Garba, yace har yanzu Gidauniyar bata nemi taimakon wasu kungiyoyi ba, ko masu hannu da shuni ba, saboda duk wanda yake bukatar tallafawa marayu da marasa hali, kofarsu a bude take,a duk inda suke ba za su rasa mabukata ba.
Haka zalika yace,suna yin hakan ne,saboda karawa sauran Alumma da kungiyoyi karfin gwiwa da wayar da kan jama,a ta hanyar shiga gidajen rediyo da kafafen sadarwa domin fahintar da Alumma, inda yace,wannan Gidauniyar Alumma da yawane suka kafata a fadin kasar nan agazawa bayin Allah.
Al’umma da dama ne suka samu halartar taron shan ruwan a fadin jihar kano da sauran jihohin Nigeria, domin ganin an gudanar da wannan shan ruwa da Gidauniyar ta saba shiryawa Duk shekara a cikin watan Azimin watan Ramadana.