Daga Abubakar Lawan Bichi
Kungiyar Fitilar Jama’a Bichi ta raba kayan abinci na kudi sama da Miliyan biyu ga Marayu da Marasa karfi a dukka fadi Karamar hukumar Bichi na taimako Azumi watan Ramadan na wannan Shekara.
Yayin raba kayan Shugaban Kungiyar Alh. Rilwanu Idris Malikawa Garu Wanda Mataimakisa Alh Aliyu Ibrahim Bichi ya wakilta, yace Kungiyar tayi haka ne domin taimakawa Marayu da Marasa karfi a cikin al’umma.
Alh Rilwanu Idris Malikawa Garu yace an zabo Marayu da Marasa karfi da kuma Masu bukatar ta musamman daga Garuruwan dagatai Arba’in da hudu 44 dake Karamar hukumar ta Bichi domin karɓar kayan .
Fatawa: Ya halatta ayi zakkar fidda kai da Taliya Kuskus ko Indomie – Mal Ibrahim Khalil
Ya kuma ya baiwa dai-daikun jama’a bisa tallafi na kudi ko kayan abinci da suka bayar domin samun Nasara shiri.
Shugaban ya kara da cewar kungiyar ta Fara tsari ciyarwa na shekara ga Marasa Lafiya da kwance a Babba Asibiti Bichi har zuwa Karshe wata Azumi Ramadan.
Wasu daga ciki Wanda suka amfana da shiri sun ya bawa Kungiya bisa Samar da taimako Azumi tun Shekaru Uku da suka gabata.
Kayanyaki abinci da aka raba sun hada Shikafa, Gero da taliya.