Za a fara allurar rigakafin cutar Maleriya a Nigeria

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

 

Gwamnatin tarayya ta amince da fara amfani da allurar riga-kafin zazzabin Maleriya wanda Jami’ar Oxford da ke Birtaniya ta samar.

 

Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta kasa NAFDAC ce ta ba da izinin amfanin da riga-kafin duk da cewa Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) da sauransu ba su kammala bincike kan rashin hadarinsa ga dan Adam ba.

Fatawa: Ya halatta ayi zakkar fidda kai da Taliya Kuskus ko Indomie – Mal Ibrahim Khalil

Da haka Najeriya ta zama kasa ta biyu a nahiyar Afirka da ta amince da riga-kafin, bayan kasar Ghana.

 

Rahoton WHO ya nuna a shekarar 2021 Najeriya ce kasar da ke dauke da kashi 27% na masu maleriya da kuma kashi 32% na wadanda ta yi sanadin mutuwarsu a duniya.

A ganinka samar da allurar rigakafi shine zai kawar da zazzabin a Nigeriya?

Wacce hanya kuke ganin ya kamata abi wajen kawar da Maleriya a kasar nan

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kotu a Kano ta hukunta masu shago saboda zubar da shara a kan titi

Kotun tafi da gidanka da ke Kano ta yanke...

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama mata da maza da ke aikata badala

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama mata hudu...

Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Magantu Kan Batun Sheikh Abduljabbar

Hukumar Gyaran Hali ta Jihar Kano ta bayyana cewa...

Dalilin da ya sa na bar tafiyar Kwankwasiyya – Farouk Lawan

Tsohon ɗan majalisar tarayya, Farouk Lawan, ya bayyana cewa...