Daga Kamal Yakubu Ali
Cibiyar tallafawa Marayu ta Dakta Adam Kamaluddeen na ma’aji ta samar
da kayayyakin sallah ga marayu maza da mata kimanin 100 da suka fito daga unguwannin Maramara, Alfindiki da kududdufawa don tallafa musu da kuma rage musu radadin halin maraici da suka tsinci kansu.
Shugaban cibiyar Dakta Adam Kamaluddeen Adam na Ma’aji ya bayyana cewa ana samar da kayayyakin ne domin tallafawa Marayun dake yankin, kasancewa sun rasa mahaifansu adon haka yace suna da hakki akan sauran al’umma wajan ganin sun basu gudunmawar da ta dace, domin sanya farin ciki a rayuwarsu.
Shugaban cibiyar yace sun fara gudanarda da rabon kayayyakin tallafin ne kimanin Shekaru uku, Kuma ya bada tabbacin zasu gaba da tallafawa marayun a lokuta irin wannan da ma sauran lokuta.
Bankwana: Gwamna Ganduje ya nemi afuwar al’ummar jihar kano
Kimanin marayu 100 maza da mata ne suka Amfana da tallafin kayan sallah , wanda ya hadar da atamfofi da Yaduka wanda cibiyar ta raba musu domin rage musu radadi da kuma ganin ta taimakawa wadanda iyayen su suka rasu.
Ku daina yiwa Masu kudin cikin ku hassada – Sheikh Abdulwahab Abdullah ya fadawa talakawa
Dr Adam ya bayyana cewa tallafawa marayu yana daga cikin ayyukan da Allah yake farin ciki dashi, hakanne yasa cibiyar take zage damtse wajan ganin ta gudanarda Rabon kayayyakin ga Marayun dake yankin.
Daga cikin Marayun da. Suka amfana da tallafin kayayyakin sun hadarda Arifullah isah da zainab Yahya sun bayyan farin cikinsu dan gane da yadda aka tallafawa rayuwarsu.
Wakilin kadaura24 ya bamu labarin cewa taron ya gudana a farfajiyar makarantar Kamaluddeen islamiyya dake unguwar marmara a karamar hukumar Birni.
Taron ya samu halarta malam Garba Adam na. Ma aji da Alhaji magaji lawam da malam Tijjani Alfindiki wakilin shugaban karamar hukumar birni malam Hafiz s Muhammad da sauran alumma da dama.